Gwamnatin Yuganda ta rufe wata gidauniyar Turai
February 3, 2021Museveni ya ce, gidauniyar na amfani da kudaden don cimma manufarta a maimakon amfanin 'yan kasa da aka ce an yi dominsu. Shugaban da ya lashe zaben shugaban kasar mai cike da cece-kuce, ya ce ba da izinin gwamnatinsa aka samar da gidauniyar da yanzu haka ake da kudi fiye da fam miliyan 100 a ciki ba, tuni ya bayar da umarnin samar da kwamitin binciken da ya kunshi 'yan Yuganda zalla.
Amma masu fashin baki na ganin matakin ka iya haifar da rikici a kasar da aka samu rabuwar kanu kan shugabancin Museveni na fiye da shekaru talatin. A shekarar 2011 ne dai, aka kaddamar da gidauniyar mai suna Democratic Governance Facility ko DGF, da zummar inganta aiyukan gwamnati da ma wadanda ba na gwamnati ba, inda batun bai wa kowanne dan kasa 'yanci ya fi samun fifiko. Kasashen Denmark da Sweden da Ireland da Austiriya da Norway da Netherlands sai kuma Britaniya da Kungiyar tarayyar Turai ne ke zuba kudaden a gidauniyar.