Shugaba Nicolas Sarkozy na Faransa na ziyara a Berlin
October 9, 2011Talla
A wannan Lahadin ne shugabanin Faransa da Jamus suke gudanar da wani taron koli a birnin Berlin na nan Jamus domin su cimma matsaya dangane da shirinsu na zuba jari a bankunan Nahiyar sakamakon fargabar samun koma bayan tattalin arziki. Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel zata gana da shugaba Nicolas Sarkozy kasancewar wasu daga cikin bankunan na Turai na fama da rikicin bashi abun da ya a yanzu haka ya kai rikicin Girka makura. A jajibirin taron kolin na Berlin. shugabar asusun bada lamuni na duniya Christine Legarde wacce ta fara yin kira da a zuba jari a bankunan ta gana da shugaban na Faransa a birnin Paris.
Mawallafiya: Pinado Abdu
Edita: Mohammad Nasiru Awal