Shugaba Nicolas Sarkozy ya gana da Shugaba Mahmud Abbas
September 27, 2010Shugaban Fararansa Nicolas Sarkozy ya ce zai karɓi baƙuncin shugabanin Israela da na Palasɗinu a wata mai kamawa. Sarkozy ya bayyana haka ne a yayin da yake neman ƙasashen turai da ma ƙasashen da ke tekun Meditaranean da su taka rawan gani wajen samar da zaman lafiya a yankin gabas ta tsakiya.
Shugaba Sarkozy,|wanda a yau ya karɓi baƙuncin shugaba Mahmud Abbas na Palasɗinu, ya nemi ya san makomar tattaunawar samar da sulhu a yankin ta gabas ta tsakiya da aka riga aka fara, ya kuma buƙaci a sake ɗage wa'adin gine-ginen Israela da aƙalla watani ukku zuwa huɗu.
Daga bisani dai Sarkozy ya ce Abbas, da shugaban Israela Benjamin Netanyahu da shugaban Masar Hosni Mubarak za su ziyarci Paris a watan Oktoba domin yin shirin wani taron ƙoli na ƙasashen tekun Meditarenean da za'a gudanar a watan Nuwamba. Mawallafiya: Pinaɗo Abdu
Edita: Umaru Aliyu