Shugaba Putin na ziyara a Mariupol
March 19, 2023Talla
A karon farko tun bayan kaddamar da mamaya a Ukraine, shugaba Vladmir Putin na Rasha ya kai ziyara yankin Donbas da dakarunsa suka mamaye. Ziyarar na zuwa ne bayan wata da ya kai yankin Crimea a jiya Asabar, kwana guda bayan da kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ICC ta tura da sammacin kama shi.
Kakafen yada labaran Rasha sun ruwaito cewa ya kewaya birnin Mariupol cikin mota tare da zantawa da mazauna yankin. Birnin na Mariupol da ya fada hannun Rasha a watan Mayun bara na kasance nasara ta farko da Rashar ta samu bayan da ta gaza kwace Kyiv babban birnin Ukraine. Kafafen yada labaran kasar sun kuma ruwaito cewa, shugaba Putin zai gana da babban hafsan sojan rundunarsa na Ukraine.