Shugaba Putin ya gana da 'yan adawan Siriya
February 25, 2016Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya gana da manyan masu ruwa da tsaki a rikicin kasar Siriya ciki kuwa har da shugaba Bashar Al-Assad da 'yan adawa, ganawar da ke zuwa bayan da ake bayyana cewa batun tsagaita wutar da Rasha da Amirka suka jagoranta zai fi zama mai amfani ne ga gwamnatin ta Siriya.
Dakarun sojan kasar ta Siriya da ke samun goyon bayan na kasar Rasha sun mamaye yankin Kudu maso Gabashin birnin Aleppo daga hannun mayakan na IS, yayin da masu tsatstsauran ra'ayin a ranar Talata ke ci gaba da iko da garin Khanaser da tsaunikan da ke kewaye da shi ta yadda suka katse hanyar da za ta dangana da birnin na Aleppo.
Majalisar Dinkin Duniya dai ta bayyana a ranar Laraba an samu dama ta kai kayan agaji mai nauyin metrik tan 21 a garin Deir el-Zour wanda mayakan na IS suka yi wa kawanya. Da misalin karfe sha biyu na daren Jumma'a ne dai a kasar ta Siriya ake sa ran shirin tsagaita wutar ya fara aiki. Sai dai abin ba zai shafi mayakan IS da reshen al-Nusra na Al-Ka'ida ba, da sauran wadanda Majalisar Dinkin Duniya ta bayyanasu a matsayin 'yan ta'adda.