1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

ANC: Sake bai wa Ramaphosa shugabanci

Lateefa Mustapha Ja'afar
December 16, 2022

Jam'iyya mai mulki a Afirka ta kudu ANC ta kaddamar da wani taro da ake sa ran zai sake zabar Shugaba Cyril Ramaphosa a matsayin shugabanta, duk da zargin badakalar kudi da ta zubar masa da mutumci.

Afirka ta Kudu |  Cyril Ramaphosa | Shugaba | ANC
Shugaba Cyril Ramaphosa dai, ya fuskanci kalubalen zargin badakalar kudiHoto: Jerome Delay/AP/dpa/picture alliance

Rahotanni sun nunar da cewa wakilan mambobin jam'iyyar ta ANC mai mulki a Afirka ta Kudun dubu hudu da 500 daga sassan kasar dabam-dabam, na shirin kada kuri'a a yayin taron na kwanaki biyar da ke gudana a wani wajen taro kusa da birnin Johannesburg. Shugaba Cyril Ramaphosa na neman yin tazarce a shugabancin jam'iyyar ta ANC, a daidai lokacin da take fuskantar kalubale sakamakon raguwar magoya baya da ta ke fuskanta bayan tsahon shekaru 28 tana mulki a kasar.