1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Ramaphosa zai sake tsayawa takara a zaben 2024

Ramatu Garba Baba
December 19, 2022

Shugaba Cyril Ramaphosa ya lashe zaben da ya ba shi damar sake tsayawa takarar shugaban kasar Afirka ta Kudu da zai gudana a shekarar 2024.

Shugaba Cyril Ramaphosa
Shugaba Cyril RamaphosaHoto: Jerome Delay/AP/dpa/picture alliance

Magoya bayan Shugaba Cyril Ramaphosa sun mamaye birnin Johannesburg don nuna farin-cikinsu kan nasarar da ya samu bayan da jam'iyyarsa ta ANC ta amince da shi a matsayin dan takararta a zaben da ya gudana a karshen makon da ya gabata. Ramaphosa ya yi nasarar doke babban abokin hamayyarsa Zweli Mkhize. 

A jawabinsa bayan wannan nasarar, ya ce, ba zai gaza ba, zai ci gaba da yakar cin hanci da rashawa da magance babbar matsalar karancin wutar lantarki da ta hana ruwa gudu. A makon da ya gabata, Ramaphosa ya tsallake rijiya da baya, bayan yunkurin tsige shi daga mukaminsa kan zargin cin hanci da kuma wasu makudden kudade da aka gano a gonarsa.