1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaba Saleh na Yemen na shirin komawa gida

June 17, 2011

Jam'iyar Yemen da ke riƙe da madafun ikon ƙasar ta nunar da cewar nan da 'yan kwanaki masu zuwa ne shugaba Ali Abdallah saleh zai koma gida domin ci gaba da harkokin mulki.

Shugaba Yemen Ali Abdallah Saleh lokacin ya ke da cikekken lafiyaHoto: AP

Jami'an Ƙasar Yemen sun bayyana cewar shugaba Ali Abdallah saleh da ke kwance a wani asibitin Saudiyya na shirin dawo gida domin ci gaba da gudanar da harkokin mulki. Wani mai magana da yawu jam'iyar da ke riƙe da madafun ikon ƙasar ne ya nunar a cikin wata hira da yayi da tashar tebebijin ta al arabiya cewar Shugaba saleh na ci gaba da murmurewa daga rauni da ya ji lokacin da aka kai hari a fadarsa makwani biyun da suka gabata. Wannan shelarta zo ne a daidai lokacin da ake samun bayanai masu saɓa wa juna game da lafiyar shugaban ƙasar Ta Yemen.

Ita dai ƙasar Amirka ta nunar da cewar Ali Abdallah Saleh da ke kunne uwar shegu game da bukatar sauka daga karaga yana fama da munannan raunuka. yayin da magoya bayansa ke nunawa cewar ƙuna ce da bata taka kara ta karya ba ya ke fama da ita. Sai dai kuma a wannan juma'ar ma, masu zanga-zangar neman sauyi sun sake fantsama akan tituna bayan sallar juma'a domin tilasawa mataimakin shugaban ƙasa da ke riƙon gado Abd Rabo Mansur yin murabus, tare da miƙa iko ga 'yan adawa.

Mawallafi: Mouhamadou Awal

Edita: Yahouza Sadissou Madobi