1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaFaransa

Shugaba Sarkozy ya tsinci Talatarsa a Laraba a Faransa

Abdoulaye Mamane Amadou
September 25, 2025

Nicolas Sarkozy zai kasance shugaban kasar Faransa na farko a tarihi da ya fuskanci hukuncin dauri a gidan yari,bayan kotu ta same shi da aikata laifi

Tsohon shugaban kasar Faransa Nicolas Sarkozy a harabar kotu
Tsohon shugaban kasar Faransa Nicolas Sarkozy a harabar kotu Hoto: Bertrand Guay/AFP/dpa/picture alliance

Kotu a Faransa ta yanke wa tsohon shugaban kasar Nicolas Sarkozy, hukuncin daurin shekaru biyar a gidan yari, bayan samun sa da laifin barin wasu da ke karkashin ikonsa neman tallafin kudin yakin neman zabe daga gwamnatin marigayi Muammar Kadhafi na Libiya a shekarar 2007.

Ci gaban shari'ar tsohon shugaban Faransa

Mai shekaru 70 a duniya da kuma ya yi mulki daga 2007 zuwa 2012, Niclas Sarkozy da zai kasance shi ne shugaban Faransa na farko a tarihi da zai fuskanci dauri a gidan yari, bisa zarginsa da aikata mummunan laifuka ciki har da na cin hanci.

A yanzu tsohon shugaban na da izinin daukaka kara kan nan zuwa tsakiyar watan Oktoba, to amma sai dai ofishin mai gabatar da kara ya bayyana cewa zai sanar da Sarkozy ranar da zai kai kansa gidan yari.

Tsohon shugaban Faransa ya rasa wata daraja ta kasa

Shugabar kotun birnin Paris, Nathalie Gavarino, ta bayyana cewa an kama Sarkozy ne da aikata laifin barin wadanda ke karkashin ikon sa, su nemi tallafin kudi daga gwamnatin Libiya, da nufin yakin neman zabensa da ya ba shi nasara.