1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Shugaba Tchiani ya yi magana da Putin

Gazali Abdou Tasawa M. Ahiwa
March 27, 2024

A karon farko shugaban kasar Nijar ya tattauna ta wayar tarho da shugaban kasar Rasha a wani mataki na kara kusantar kasashensu da karfafa huldar dangantaka a tsakaninsu musamman a fannin tsaro da na tattalin arziki.

Niger | General Abdourahmane Tchiani
Hoto: CNSP

Gidan Talabijin na kasar ta Nijar ya nuno shugaban kasar Janar Abdourahmane Tchiani rike da wata wayar tarho ta girke ta ofishinsa sanye da kakinsa na soja kewaye da wasu mukarrabansa, yana tattaunawa kai tsaye cike da alfahari da takwaransa Vladmir Putin na kasar Rasha.

Ko da yake cewa sun saka labule a muryar tasu, amma gidan talabijin na gwamnatin kasar ya ruwaito cewa bayan yi wa juna ta'aziyya a game da hare-haren ta'addanci da kasashen biyu suka fuskanta a baya bayan nan, shugabannin biyu sun tattauna a kan batun karfafa huldar kasashen nasu biyu a fannin tsaro da tattalin arziki kafin daga karshe Shugaba Tchiani ya gode wa Shugaba Putin dangane da goyon bayan da yake kawo wa Nijar a gwagwarmayarta ta neman cikakken ‘yancin kanta.

Shugaba Vladimir Putin na kasar RashaHoto: picture-alliance/AA/Russian Presidential Press and Information Office

Wannan kusantar juna da kasashen Rasha da Nijar ke yi na zuwa ne a daidai loakcin da huldar Nijar da Amurka da kuma kasashen Turai ke kara tabarbarewa.

Wannan mataki na fifita dangantaka da Rasha da mahukuntan Nijar ke yi a kan kasashen Turai da Amurka ya haifar da mahawara a tsakanin ‘yan kasar kan alkhairi ko akasi da ke tattare da matakin.

Za a iya cewa dai sannu a hankali kasar Rasha na kara samun gindin zama a kasashen Sahel wadanda wasu ke kallo a matsayin sabon yakin cacar baka da aka shiga tsakanin Rasha da Amurka da sauran manyan kasashen yamma.