Tinubu ya janye 'yan sanda da ke kare manya
November 24, 2025
A cewar ofishin shugaban na Najeriya, Shugaba Bola Tinubu ya ba da umarnin a dauki dubban sabbin jami'an 'yan sanda saboda tsananin matsalar tsaro da ake ciki a kasar a halin yanzu.
Shugaba Tinubu na fuskantar matsin lamba tun bayan gakuwar da aka yi da kusan mutum 400, fiye da 300 daga cikinsu dalibai.
Wannan shi ne guda daga cikin mafi munin hare-haren garkuwa da mutane da suka faru a Najeriyar a baya-bayan nan.
Gwamnatin Bola Tinubu na karkashin sa ido sosai tun bayan da shugaban Amurka Donald Trump ya yi barazanar daukar matakin soja a kan Najeriya a wannan watan na Nuwamba, kan abin da ya kira kisan Kiristoci da masu tsattsauran ra'ayi cikin Musulmai ke yi a Najeriya.
Shugaba Tinubun dai ya amince da daukar karin jami'an 'yan sanda akalla dubu 30 ne a kasar.
Wani rahoto da hukumar ba da mafaka ta Tarayyar Turai ta fitar a watan jiya, ya ce fiye da 'yan sanda 100,000 daga cikin dubu 371, na aikin tsaron 'yan siyasa ne da manyan mutane, ba ayyukan da suka shafi talakawa kai tsaye ba.