Shugaba Trump da mai dakinsa sun sha ihu a wurin taro
June 12, 2025
Cincirundon jama'a ne suka yi wa shugaban Amurka Donald Trump ihu, lokacin da ya halarci taron farko na kaddamar da cibiyar bunkasa al'adu da horas da matasa raye-raye ta John F. Kennedy, yayin da wasu magoya bayansa kuma suka jinjina masa.
Mr. Trump tare da mai dakinsa Melania, sun fuskanci fushin mahalarta taron ne sakamakon matakin da ya dauka na rushe wasu hukumomin gwamnati, wasu kuma ya dakatar da tallafa musu da kudi, wadanda suka shafi harkokin tarihi da al'adu, a kokarinsa na yin kwaskwarima ga tsarin gudanar da mulkin Amurka, lamarin da ya jefa kasar cikin rudani da zazzafan maratani.
Karin bayani:Jami'an tsaro sun afka wa masu zanga-zanga a Amurka
Yanzu haka dai zanga-zanga ta barke a wasu sassan Amurka, don nuna rashin amince wa da manofifn gwamnatin shugaba Trump, musamman batun korar bakin haure 'yan ci-rani.