SiyasaGabas ta Tsakiya
Shugaba Trump na duba yiwuwar sassauta wa Iran takunkumi
June 25, 2025
Talla
Shugaba Donald Trump na Amurka na duba yiwuwar sassauta wa Iran takunkuman da kasarsa ta kakaba ma ta, domin ba ta damar sake gina kasar, tare da farfado wa daga mawuyacin halin da ta shiga.
Mr Trump wanda ya yi wannan jawabi yayin babban taron kawancen kungiyar tsaro ta NATO, ya ce Iran na bukatar samun kudaden shiga ta hanyar sayar da man fetur din da take hako wa.
Karin bayani:Iran ta musanta sanarwar Trump ta tsagaita wuta da Isra'ila
Wannan na zuwa kwana guda bayan da ya bayyana amicewarsa ta sahale wa China sayen man Iran, jim kadan da cimma masalaha kan yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Iran da Isra'ila.