Birtaniya: Zanga-zanga kan ziyarar Trump
July 13, 2018Talla
Yayin wannan ziyara Firaministar Birtaniyan Theresa May da shugaban Amirka Donald Trump sun ziyarci makarantar horar da sojoji da ke Birtaniya a Sandhurst, kafin daga bisani su dawo fadar gwamnatin, inda May za ta yi wa Trump karin haske kan tsare-tsaren da take bi masu sassauci, na kammala ficewar Birtaniya daga kungiyar Tarayyar Tuari EU. Tun da farko yayin hira da wata jarida, Trump ya ce in har May ta yi amfani da tsarin nata, dangantakar da ke tsakanin Birtaniya da Amirka ka iya zuwa karshe. May da Trump sun gana a wani wuri da ke gefen Ingila, inda daga bisani Trump zai kai ziyara ga sarauniyar Ingilan Elizabeth ta II.