1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaba Trump ya janye shirin kai hari a cibiyar wutar Iran

March 23, 2026

Shugaba Trump ya janye shirin kai hari kan cibiyar wutar Iran bayan tattaunawar kawo karshen yaki da suka kaddamar kan Iran din tare da Isra'ila. Sai dai ma'aikatar harkokin wajen Iran ta musanta cewa ana tattaunawa.

Shugaban Amurka Donald Trump yana yi wa manema labarai bayani a Washington
Shugaban Amurka Donald Trump yana yi wa manema labarai bayani a WashingtonHoto: Brendan Smialowski/AFP/Getty Images

Shugaban Amurka, Donald Trump, ya tsawaita wa'adin da ya bai wa Iran na bude mashigin ruwan Hormuz, inda ya jinkirta yiwuwar kai hare-hare da kwanaki biyar.

Trump ya ce an gudanar da tattaunawa mai kyau a tsakanin bangarorin biyu tare da nuna fatan warware rikicin, kuma za a ci gaba da ganawa a cikin wannan makon.

Sai dai ma'aikatar harkokin wajen Iran ta musanta cewa ana wata tattaunawa.

Kafafen yada labaran Iran din sun ce jinkirin alama ce ta cewa Amurka ta ja da baya, bayan gargadi daga Tehran.

Rikicin, wanda ya shiga mako na hudu, ya riga ya yi sanadin mutuwar sama da mutane dubu biyu, kuma na ci gaba da barazana ga samar da makamashi da zaman lafiyar yankin.