1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Shugaba Trump ya yi barazanar sake far wa Iran da yaki

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
April 10, 2026

Mr Trump ya ce dakarunsa sun shirya tsaf, don tarwatsa Iran, fiye da yakin da ya gabata, bayan sake zage damtse.

Shugaba Donald Trump na Amurka
Shugaba Donald Trump na AmurkaHoto: Brendan Smialowski/AFP

Shugaba Donald Trump na Amurka ya yi barazanar yin amfani da jiragen ruwa na yaki, wadanda ke makare da makamai, don kai wa Iran farmaki, matukar tattaunawar yarjejeniyar cimma sulhun tsagaita wuta a kasar Pakistan ta gaza cimma nasara.

Karin bayani: Isra'ila ta ce za ta yi tattaunawar sulhu da Lebanon

Mr Trump na wannan jawabi ne a tattaunawa da jaridar New York Post a wannan Juma'a, yana mai cewar dakarunsa sun shirya tsaf, don tarwatsa Iran, fiye da yakin da ya gabata, la'akari da zage damtse da suka yi.

Karin bayani:Iran ta ce ba za ta takaita shirin kara karfin Uranium dinta ba

Tuni mataimakinsa JD Vance ya kama hanyar zuwa birnin Islamabad a Juma'ar nan, domin wakiltar Washington, a zagayen farko na tattaunawar lalubo bakin zaren dakatar da yakin, biyo bayan amincewar da kasashen biyu suka yi ta tsagaita wuta ta tsawon makonni biyu.