1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaba Zelensky na Ukraine na halarta taron G7

Binta Aliyu Zurmi
May 20, 2023

A wata ziyarar ba zata, Shugaba Volodmyr Zelensky na kasar Ukraine ya isa Japan inda shugabannin kasashen duniya mafiya karfin tattalin arziki ke babban taro, batun kasar Ukraine shi ne ya mamaye zauren taron.

G7 Gipfel in Japan, Hiroshima | Wolodymyr Selenskyj trifft Giorgia Meloni
Hoto: Ludovic Marin/POOL/AFP/Getty Images

Taron da Zelensky ya kamata ya halarta ta kafar bidiyo na da zummar tattaunawa da shugabannin kungiyar G7 don neman karin goyon bayansu na ladabtar da Rasha bisa mamayar da take ci gaba da yi a kasarsa watanni 15.

Sabbin takunkuman da aka laftawa Rasha sun hada da katse duk wasu hanyoyi da ta ke samun kayayakin soji, gami da dakile hanyoyin da Rasha ke samun kudaden shiga ciki har da fitar da makamashi zuwa kasashen ketare da ma sayar da ma'adanan karkashin kasa na lu'u-lu'u

Kazalika akalla hukumomi 70 a Rasha da wasu kasashe masu alaka da ita za a haramta wa samu da ma sayen kayayyakin da Amurka ke fitarwa.


Amurka wacce ke gogon bayan Ukraine tuni ta amince da samarwa Ukraine jiragen yaki samfurin F-16.