1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaba Zelenskyy ya ce Ukraine na nan daram

December 22, 2022

Shugaba Volodymyr Zelenskyy na kasar Ukraine, ya fada wa majalisar dokoki a Amirka cewa kasarsa na nan daram duk kuwa da yakin nan da Rasha ta kaddamar a kanta.

Shugaba Volodymyr Zelenskyy na kasar Ukraine
Shugaba Volodymyr Zelenskyy a majalisar dokokin Amirka Hoto: Carolyn Kaster/'AP Photo/picture alliance

Shugaba Zelenskyy ya gabatar da jawabi ne a gaban 'yan majalisar Amirka, jim kadan bayan kammala taron manema labaru da suka yi da Shugaba Joe Biden.

Shugaban na Ukraine ya ce kasarsa ta samu galaba a kan Rasha a yakin da take yi a madadin kasashen duniya.

Wannan ne ziyarar farko da Shugaba Zelenskyy ya kai wata kasar duniya, tun lokacin da Rasha ta afka wa kasar cikin watan Fabrairu.

Daga nashi bangare, Shugaba Joe Biden na Amirka, ya ce kasarsa na tare da Ukraine kuma za ta ci gaba da taimaka mata a halin da ta samu kanta.

Mr. Biden ya kuma yi alkawarin bai wa Ukraine karin tallafi na tsaro da ya kai na dala biliyan daya da miliyan 800, ciki har da wasu sabbin makaman kare kai masu linzami.