1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaban ƙasar Faransa na tattaunawa da Angela Merkel

October 19, 2011

Shugabannin biyu na koƙarin samar da hanyoyin magance matsalar tattalin arziki da ƙasashen ƙungiyar Tarrayar Turai ke fuskanta gabanin babban taron da za'a yi a ƙarshen mako

Angela Merkel tare da Nicolas SarkozyHoto: dapd

Shugaban ƙasar Faransa Nicolas Sarkozy ya yadda zango a birnin Francfort da ke a nan tsakiyar ƙasar Jamus;inda zai halarci wani taron gauggawa na share fage ga babban taron ƙungiyar Tarrayar Turai da za a gudanar ran lahadi a birnin Brussels na ƙasar Beljium domin tattauna matsalar tattalin arziki da ƙasashen ƙungiyar ke fama da ita.

Sarkozy wanda zai sadu da shugabar gwamnatin jamus Angela Merkel a birnin na Francfort inda nan ne cibiyar banki Tarrayar Turai tare kuma da wasu sauran hukumomin kudi na ƙungiyar.Zasu tsara shirin da za su gabatar ga babban taron da za a yi nan gaba domin samar da hanyoyin da za su zama mafita ga rikicin kuɗi na ƙasashen.Tun can da fari a taron da shugabannin biyu suka yi a birnin Berlin Merkel da Sarkozy sun yi alƙawarin gabatar da sahihan shawarwari ga babban taron na ƙungiyar Tarrayar Turai.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Zainab Moahammed Abubakar