1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaban ƙasar Masar ya naɗa Firaminista

July 24, 2012

Hisham Kandil ministan noman rani mai barin gado ya zama saban Firaministan Masar

epa03316039 A Handout photograph released by the Egyptian Presidency on 21 July 2012, shows Egyptian President Mohamed Morsi meeting with Hisham Qandil, at the presidential palace, in Cairo, Egypt, 21 July 2012. According to media reports on 24 July 2012, Egyptian President Morsi appointed Minister of Water and Irrigation Hisham Qandil as Prime Minister on 24 July and asked him to form a new government, a presidential spokesman said according to state media. EPA/EGYPTIAN PRESIDENCY/HANDOUT HANDOUT EDITORIAL USE ONLY/NO SALES +++(c) dpa - Bildfunk+++
Hisham Kandil na ganawa da shugaban ƙasaHoto: picture alliance/dpa

Shugaban ƙasar Masar Mohammad Mursi ya naɗa Hisham Kandil ministan noma rani mai barin gado a matsayin saban Firaminista.Qandil mai shekaru 50 a duniya, injiniya ne ta fannin harkokin noma.Yayi karatu a jami'ar birnin Alƙahira da kuma Caroline ta Arewa a ƙasar Amurika.

Ya riƙe manyan muƙammai a ofishin ministan dake kula da noma kamin daga bisani ya zama minista.Tun lokacin yaƙin neman zaɓe shugaba Mohammad Mursi ya yi alƙwarin naɗa Firaminista da zai samu karɓuwa daga jama'a, wanda ya samu cikkakar shaida ta fannin kishin ƙasa da nuna adalci.

A kwanaki masu zuwa Hisham Kandil zai gabatar da ministoci, a yanzu jama'ar ƙasa ta zuba ido ta ga ko gwamntai za ta ƙunshi ɓangarori daban-daban na jama'ar ƙasa ko kuma membobin jam'iyar 'yan uwa muslumi za su kalkace ta.

Mawallafi:Yahouza Sadissou Madobi
Edita:Saleh Umar Saleh