1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Joe Biden: Babu yiwuwar tsagaita wuta a Gaza

Abdourahamane Hassane
November 9, 2023

Biden ya bayyana haka dab da lokacin da Jami'an leken asirin Isra'ila da na Amurka ke tattaunawa da jami'an Qatar a birnin Doha kan batun tsagaita wutar saboda ayyukan jin kai.

 Joe Biden
Joe BidenHoto: Matt Rourke/AP/picture alliance

Biden wanda daman yake yin adawa da tsaigata wutar ya yi wannan furci dab da lokacin da Jami'an leken asirin Isra'ila da na Amurka ke tattaunawa da jami'an Qatar a birnin Doha kan batun tsagaita wutar saboda ayyukan jin kai. Daraktan CIA Bill Burns da Shugaban hukumar leken asiri na Isra'ila  Mossad David Barnea dukkansu suna a birinin Doha, domin  tattaunawa da shugabannin Qatar a kan  yiwuwar tsagaita wuta da za ta kai ga sakin yan Israilan da Hamas ke yin garkuwa da su da kuma shigar da karin agaji a Gaza. A halin da ake ciki Isra'ila ta ce za ta fara tsagaita wutar na sa'o'i hudu a kowace rana a wasu yankuna na arewacin zirin Gaza, wanda za a sanar da sa'o'i uku kafin lokacin  in ji mai magana da yawun fadar White House.Gaza al'amura na yin tsanani