1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAmurka

Shugaban Amurka Joe Biden ya kamu da cutar Corona

July 18, 2024

Hukumomin kasar Amurka sun tabbatar da cewar shugaban kasar ya kamu da kwayar cutar sarkewar numfashi ta Corona, daidai lokacin da yake yakin neman zabe a ranar Laraba

Shugaba Joe Biden na Amurka
Shugaba Joe Biden na shirin tashi dag filin jirgi na Las VegasHoto: Susan Walsh/AP Photo/picture alliance

Shugaba Joe Biden na kasar Amurka, ya kamu da kwayar cutar Corona kamar yadda fadar White House ta tabbatar.

Shugaban na Amurka Biden wanda da ma ke yakin zabe a Nevada,  ya katse jawabinsa a lokacin wani taro kan kare hakkin 'yan yankin Latino.

Fadar ta White House dai ta ce, Shugaba Biden ya nuna alamun cutar da su ne suka tabbatar da cewa ya kamu, sai dai ba su yi tsanani ba.

Yanzu dai Mr. Biden zai ci gaba da gudanar da aikinsa na gwamnati ne daga gidansa da ke a Delaware.

Shugaban kasar ta Amurka mai shekaru 81 da haihuwa na kokarin nuna wa masu sukar karsashinsa a yanzu wadanda ke shakkun ko zai iya fafatawa da babban abokin hamayyarsa tsohon Shugaba Donald Trump a zaben kasar da za a yi cikin watan Nuwamba.

Ya dai nace kan cewa zai ci gaba da takarar duk da kiraye-kirayen janyewa da ake yi masa a ciki da ma wajen jam'iyyarsa ta Democrats.

Wannan dai wani kalubale ne ga Shugaba Joe Biden a siyasance.