1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaban askarawa ƙasar Masar ya yi jawabi zuwa ga al'umma

November 22, 2011

Za a gudanar da zaɓen shugaban ƙasa kafin ƙarshen watan yuni tare kuma da kafa wata gwamnatin wucin gadi wacce za ta jagorancin al'amuran ƙasar

Hussein Tantawi, shugaban askarawa na ƙasar MasarHoto: picture alliance/dpa

An cigaba da shan gumurzu a dandalin Tahriri na birnin Alƙahira da ke a ƙasar Masar,inda gomai na duban jama'ar suka yi cikar ƙwari wanda ke karwara da jamian tsaro da duwartasu wanda su kuma suke yi masu feshin hayaƙi mai sa ƙwala.masu gudanar da zanga zangar da ke ɗauke da ƙwalayan wanda ke da rubuce rubuce da ke yin suka ga babban hapsan hapsoshin sojin ƙasar ,na cewar ya sauka daga mulki.

A halin da ake ciki sojojin , sun amince a shirya zaɓen shugaban ƙasa kafin nan da ƙarshen watan yuni tare kuma da kafa wata gwamnatin riƙon ƙwarya wacce zata jagoranci al' amuran ƙasar.Kuma shugaban askarwa na ƙasar Marsharl Hussein Tantaoui wanda ke jagoranci ƙasar tun bayan juyin juya halin da ya biya da gwamnatin Hosni Moubarak ya yi jawabi zuwa ga al umma.''ya ce mun amince da marabus ɗin da gwamnatin ta yi sannan kuma ya ce zamu ɗauki duk matakan da suka dace domin kiyaye ƙasar Masar ga fadawa cikin wanin mawuyacin hali domin ƙasar ta sake komawa kan hanyar tattalin arziki na gari.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Zainab Mohammed Abubakar