Shugaban bankin duniya ya gargadi kasashen Turai
June 17, 2012Shugaban bankin duniya, Robert Zoellick ya gargadi kasashen Turai game da yadda suke rikon sakainar kashi ga rikicin kudi. Robert Zoellick ya yi wannan kiran ne gabanin shiga taron kasashen G20 da za a fara a ranar Litinin a kasar Mexico. Zoellick ya ce kasashen Turai a ko da yaushe suna sako-sako wajen daukar matakin da ya dace domin ceto kudin euro. A cikin firar da jaridar "Der Spiegel" ta yi da shi Zoellick ya soki matakin babban bankin Turai na sake neman gabatar da sabon matsayin durkushewar bankuna domin samun karin lokaci. Ya ce yin hakan ba zai warware ainihin matsalar da ke akwai ba. Shugaban bankin na duniya ya ce kasashen Turai na bukatar gaggauta daukar mataki wajen tinkarar wannan matsala.
Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas
Edita: Umaru Aliyu