1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaban bankin duniya ya ajiye aiki

Abdul-raheem Hassan
January 8, 2019

Jim Yong Kim ya ajiye mukaminsa na shugaban bankin duniya gabannin wa'adinsa a shekarar 2022 domin samun damar ci gaba da kasuwanci mai zaman kansa.

USA Weltbank l Jim Yong Kim trifft zurück
Hoto: Getty Images/A. Verdelli

Babban bankin duniya ya tabbatar da murabus din shugabansa Jim Yong Kim shekaru uku gabannin wa'adin shugabancinsa a shekarar 2022. Kim ya nuna gamsuwa da kasancewa shugaban bankin duniya na tsawon shekaru, ya ce ajiya aikin zai ba shi damar maida hankali kan harkokin kasuwanci da zuba jari a kasashe masu tasowa.

A watan Yulin shekara ta 2017 ne Jim Yong Kim ya fara jan ragamar shugabancin bankin duniya karo na biyu bayan da ya gaji tsohon shugaban bankin Robert Zoellick a 2012 karkashin shugabancin tsohon Shugaban Amirka Barack Obama.

A ranar 1 ga watan Fabrairun shekarar 2019 ne wa'adin Kim zai kawo karshe a hukumance, yayin da Kristalina Georgieva za ta kasance mukaddashiyar shugaba. Shugaban Amirka Donald Donald Trump na da damar sake zaban wanda zai shugabancin bankin duniya nan gaba.

Tsallake zuwa bangare na gaba Babban labarin DW

Babban labarin DW

Tsallake zuwa bangare na gaba Karin labarai daga DW