SiyasaAfirka
Shugaban Chadi Mahamat Idriss Deby ya nada sabon firaminista
May 24, 2024Talla
Sabon zababben shugaban Chadi Mahamat Idriss Deby Itno, ya nada tsohon jakadan kasar a Chaina Allamaye Halina, a matsayin sabon firaminista, bayan karbar rantsuwar kama aiki na tsawon shekaru 5.
Karin bayani:Chadi: Kotu ta tabbatar da nasarar Deby
Sakataren fadar shugaban kasa Mahamat Ahmat Alhabo ne ya sanar da nadin, yayin wani jawabi ta gidan talabijijn din kasar ranar Alhamis.
Karin bayani:Takun saka kan sakamakon zaben Chadi
A baya dai jagoran adawa Succes Masra ne firamininstan wanda kuma ya fafata da shugaba Mahamat Deby a zaben shugaban kasar da ya gabata, inda ya sanar da ajiye aikinsa bayan shan kaye a zaben.