1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Shugaban Chadi zai tsaya takarar wa'adi na shida

February 6, 2021

Jam'iyya mai mulki a kasar Chadi ta sanar a wannan Asabar cewa ta tsayar da Shugaba Idriss Deby Itno a matsayin dan takararta a zaben da za a yi a watan Afrilu mai zuwa. 

Präsident Tschad - Idriss Déby Itno
Hoto: UImago/Xinhua/C. Yichen

Duk da irin yadda ake kallonsa a matsayin mai karyawa inda babu gaba, Shugaba Deby tsohon babban hafsan soja da ya mulki Chadi na shekaru 30, na ci gaba da samun goyon bayan kasashen duniya wadanda ke kallonsa a matsayin abokin tafiya a wurin yaki da 'yan ta'adda a kasar da ke yankin Sahel.

Da yake sanar da aniyarsa ta yin takara, Shugaba Deby ya ce jama'ar kasar ce ta tilasta masa neman wa'adi na shida a don haka ya amsa kiraye-kirayen 'yan kasar domin ci gaba da bayar da gudunmawarsa.

Sai dai a gefe guda wasu 'yan adawa sun so yin zanga-zanga a wannan Asabar don bijire wa takarar ta shi amma kuma hukumomi sun dakatar da su.