1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Shugaban CIA ta Amurka zai je Masar kan batun yakin Gaza

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
July 7, 2024

Mr Burns zai ziyarci Qatar, kafin daga bisani ya gana da tawagar gwamnatin Isra'ila, domin tsayar da yakin baki daya

Hoto: MANDEL NGAN/AFP/Getty Images

Shugaban Hukumar Leken Asiri ta Amurka William Burns na shirin kai ziyara Masar, don tattauna hanyoyin tsagaita wuta a yakin Gaza, kamar yadda gidan talabijin din Masar na Al Qahera ya rawaito a Lahadin nan.

Karin bayani:Isra'ila ta yi na'am da shiga tattaunawa da Hamas

Haka zalika Mr Burns zai kai ziyara Qatar, kafin daga bisani ya gana da tawagar gwamnatin Isra'ila, domin lalubo bakin zaren tsayar da yakin baki daya.

Karin bayani:Takaitacciyar tsagaita wuta za ta fara aiki a Gaza

Yakin dai ya barke ne tun bayan harin ba-zata da kungiyar Hamas mai gwagwarmaya da makamai a yankin Zirin Gaza na Falasdinu ta kai Isra'ila a ranar bakwai ga watan Oktoban bara, kuma kawo yanzu yakin ya yi sanadiyyar mutuwar Falasdinawa sama da dubu talatin da takwas.