Shugaban Colombia ya kori jami'an diflomasiyyar Isra'ila
October 2, 2025
Shugaban Colombia Gustavo Petro ya sanar da cewa ya sallami dukkan jami'an diflomasiyyar Isra'ila da suka rage a kasar, bayan sojojin ruwan Isra'ila sun tsare jirgin flotila mai dauke da kayan agajin jinkai zuwa Gaza.
Karin bayani:Zaben shugaban kasa a Kwalambiya
Shugaba Petro ya ce daga cikin 'yan gwagwarmayar da ke cikin jiragen ruwan akwai wasu mata guda biyu masu rajin kare hakkin bil Adama 'yan kasar ta Colombia, wadanda suka sadaukar da rayuwarsu domin al'ummar Falasdinawa.
Karin bayani:Kotu ta yanke wa tsohon shugaban Colombia hukuncin daurin shekaru 12
A baya bayan nan shugaban kasar Colombia ya shiga sahun masu zanga-zangar adawa da yakin Gaza a birnin New York na Amurka, inda ya yi kira ga sojojin Amurka da su bijirewa Trump. Matakin da ya sanya hukumomin Washington DC soke bizar Mr. Petro.
The Global Sumud Flotilla wani rukuni ne na jiragen ruwa makare da kayan agajin jinkai wanda kuma ke dauke da fitattun 'yan gwagwarmaya daga kasashe daban-daban ciki har da 'yar fafutukar kare muhalli ta Sweden Greta Thunberg.