1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Tattalin arzikiLatin Amurka

Colombiya ta kafa dokar ta-baci na tattalin arziki

Suleiman Babayo AH
December 23, 2025

Shugaba Gustavo Petro na kasar Colombiya ya kafa dokar ta-baci kan tattalin arzikin kasar, bayan takaddama da mahajisar dokoki kan kasafin kudi na shekara mai zuwa ta 2026.

Shugaba Gustavo Petro na kasar Colombiya
Shugaba Gustavo Petro na kasar ColombiyaHoto: Ivan Valencia/AP Photo/dpa/picture alliance

Gwamnatin kasar Colombiya ta kafa dokar ta baci kan tattalin arzikin kasar, abin da zai bai wa Shugaba Gustavo Petro damar amfani da dokokin da ya kafa kai tsaye na haraji domin magance matsalolin da ake fuskanta na samar da kudin tafiyar da asibitoci da bashin da ya yi katutu kan rundunar sojan kasar.

Dalilan kafa dokar ta-bacin

Sojojin kasar ColombiyaHoto: Schneyder Mendoza/AFP

Shugaba Petro ya kafa wannan dokar bayan dokar haraji da yake bukata ta gaza samun amincewar 'yan majalisar dokokin kasar.

A wannan shekara ta 2025 mai karewa akwai kasafin kudi na kimanin dala bilyan 134, sannan gwamnati ta kara dala bilyan hudu a kan wannan kudi a matsayin kasafin kudin shekara mai zuwa ta 2026, abin da majalisar dokoki ta saka kafa ta yi fatali da shi, saboda karin harajin da ake bukata kafin aiwatar da kasafin kudin.

Tuni 'yan kasuwa suka caccaki matakin gwamnatin kasar ta Colombiya da ke yankin Latin Amurka kan wannan dakar ta-baci a bangaren tattalin arziki.