Mali: Shugaban ECOWAS ya gana da gwamnatin rikon kwarya
October 11, 2020Talla
Shugaban ECOWAS ya samu tarabar shuzgaban rikon kwarya Bah N'daw a filin jirgi, kana ya kuma gana da mataimakin shugaban kasar Assimi Goita wanda ya jagoranci kifar da gwamnatrin tsohon shugaban Ibrahim Boukar Keita a watan Agusta.
Kungiyar raya tattalin arzikin yammacin aksashen Afirka ECOWAS ko CEDEAO sun dage takunkumi karya tattalin arzikin Mali bayan da sojiojin da suka kifar da mulkin suka amince da maida kasar karkashin mulkin farar hula zuwa lokacin shirya sabon zabe, tare da yarjejeniyar sake wadanda aka kama loakcin juyin mulkin.