1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Blinken ya gana da shugaban Falasdinawa Mahmoud Abbas

Binta Aliyu Zurmi
November 5, 2023

Sakataren harkokinn wajen Amurka Antony Blinken ya gana da shugaban Falasdinawa Mahmoud Abbas a birnin Ramallah. Sun tattauna bukatar maido da zaman lafiya a yankin.

US-Außenminister Blinken trifft Palästinenserpräsident Abbas
Hoto: PPO/AFP

Wannan ita ce ziyara ta biyu da Blinken ke kai wa yankin tun bayan da Isra'ila ta kaddamar da yaki da Hamas. Ganawar ta shafe sama da sa'o'i biyu, Blinken ya bayyana cewar ba za a tilastawa Falasdinawa barin muhallansu ba.

Shugaban Falasdinawa Mahmoud Abbas ya baiyyana tsananin takaicinsa na kin sauraren kiraye-kiryaen tsagaita wuta da Isra'ila ta yi, ya ce kisan kiyashi ta ke yi wa Falasdinawa ba tare da kiyaye dokokin kasa da kasa ba.

Kazalika Mahmoud Abbas ya bukaci dakatar da luguden wuta ba tare da wani bata lokaci ba, to sai dai tun bayan ganawarsa da shugabannin kasashen Jordan da Masar Blinken ya ce babu batun tsagaita wuta a yanzu, saboda hakan ka iya baiwa Hamas damar sake wani shiri.