1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

Shugaban Faransa na shan matsin lamba kan sabon firaminista

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
December 10, 2024

Mr Macron ne da kansa ya gayyaci shugabannin jam'iyyu don ganawa da su a kan batun amma banda guda biyu wato RN ta Marine Le Pen, da kuma LFI da suka fi rinjaye a majalisar dokokin kasar.

Firaministan Faransa mai barin gado Michel Barnier
Hoto: AFP

Shugaban Faransa Emmanuel Macron na fuskantar matsin lambar ayyana sabon firaminista nan da sa'o'i 48, bayan ganawa da jagororin jam'iyyarsa da kuma na wasu jam'iyyun a Talatar nan, biyo bayan sauke firamininsta mai ci Michel Barnier.

Karin bayani:Jam'iyyar Macron ta sha kaye a zaben 'yan majalisa

Mr Macron ne da kansa ya gayyaci shugabannin jam'iyyun, amma banda guda biyu wato National Rally RN ta Marine Le Pen, da kuma LFI, wadanda suke da rinjaye a majalisar dokokin kasar.

Karin bayani:Ana zaben 'yan majalisar dokoki a Faransa

Wannan wani yunkuri ne da Mr Macron ke yi don yayyafa ruwan sanyi ga dambarwar siyasar kasar da ta yi zafi matuka a 'yan kwanakin nan, har ta kai ga kada kuri'ar yankan kauna ga firaminista Michel Barnier, da ya zama tilas ya sauka, har ma Macron din ya amince da murabus dinsa.