Shugaban Gambiya Adama Barrow ya koma gida
January 26, 2017Talla
Barazanar sojojin na hadakar ce dai ta tursasawa tsohon shugaban kasar Yahya Jammeh ficewa daga Gambiya, inda a halin yanzu ya ke zaman gudun hijira a kasar Equatorial Guinea. Jakadan musamman na Majalisar Dinkin Duniya a yankin Afirka ta Yammam, Mohammaed Ibn Chambas ya fada a Dakar babban birnin kasar senegal cewa, bukatar tsawaita zaman dakarun a Gambiya wani lamari ne da ake ganin zai inganta tsaron kasar da ake wasu-wasi a kansa.
A yau Alhamis ne dai sabon shugaban na Gambiyan Adama Barro ya koma zuwa kasar ta sa tun bayan rantsar da shi da aka yi a kasar Senegal, a ranar 19 ga wannan wata na Janairu da muke ciki sakamakon kememen da Yahya Jammeh ya yi tun farko.