1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Shugaban Gambiya ya samu nasara karo na biyu

Abdul-raheem Hassan SB
December 6, 2021

Hukumar zaben kasar Gambiya ta ba da sakamakon zaben da ya tabbatar Shugaba Adama Barrow ya sake lashe zaben shugaban kasar da ya wakana a karshen mako inda ya samu sabon wa'adi na biyu na mulki.

Gambia | Wahlen 2021 | Amtsinhaber Adama Barrow Wahlsieger
Hoto: Leo Correa/AP Photo/picture alliance

Shugaban kasar Gambiya mai ci Adama Barrow ya samu nasarar zama shugaban kasa karo na biyu a zaben da ya gudana a karshen mako, hukumar zaben kasar ta ce Barrow ya doke abokan karawarsa a zaben da yawan kuri'u kashi 53 cikin 100.

To sai dai tuni babban dan takara na bangaren adawa Ousainou Darboe wanda ya samu kaso 28% cikin 100 na yawan kuri'un ya yi watsi da sakamakon zaben, amma tuni magoyan bayan Shugaba Adama Barrow suka karade titunan babban birnin kasar Banjul da murna.

Barrow wanda mulkinsa na shekarun biyar na farko ya kawo karshen shugabancin kama-karya na tsohon shugaban kasar Yaya Jammeh na fiye da shekaru 20, ya yi alkawarin amfani da dukiyar kasar wajen shawo kan matsalolin da suke ciki.