1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaban gwamantin Jamus ya kammala ziyararsa a China

Zainab Mohammed Abubakar
February 26, 2026

Bayan ganawa da Shugaba Xi Jinping da kuma sanar da yarjejeniyar Airbus, Friedrich Merz ya kammala rangadin aikin kwanaki biyu da ya kai China da ziyara a cibiyar fasaha ta Hangzhou.

Hoto: Michael Kappeler/REUTERS

 

Ziyarar Merz ta farko a hukumance a China, ta zo ne a daidai lokacin da Berlin da Beijing ke neman gina dangantaka mai dorewa, a yayin da duniya ke cikin yanayi na rashin tabbas a fannin tattalin arziki, sakamakon takunkumin harajin da manufofin ketare na shugaban Amurka Donald Trump.

China, wacce ita ce kasa ta biyu a duniya a bunkasar tattalin arziki, ta zarce Amurka a bara don zama babbar abokiyar cinikayya ta Jamus. A lokaci guda kuma, Berlin ta dauki kasar da jam'iyyar kwaminisanci ke jagoranta, a matsayin abokiyar hamayyar tsarin mulki ga kasashen yamma.

Shugaban gwamnati Merz ya samu rakiyar manyan 'yan kasuwa, ciki har da shugabannin manyan kamfanonin kera motocin Volkswagen, da BMW da kuma  Mercedes.