1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus na son karfafa alaka da Isra'ila

December 6, 2025

Shugaban gwamnatin Jamus, Friedrich Merz za kai ziyarar aiki zuwa Isra'ila a wani mataki na kara karfafa alaka tsakanin Jamus da Isra'ila da ta yi tsami a lokacin yakin Gaza.

Shugaban gwamnatin Jamus, Friedrich Merz da Firanminstan Isra'ila Benjamin Netanyahu
Shugaban gwamnatin Jamus, Friedrich Merz da Firanminstan Isra'ila Benjamin NetanyahuHoto: Kobi Gideon/GPO/dpa/picture alliance

Gabanin ya isa Isra'ila, Friedrich Merz ya tsaya a Jordan domin ganawa da sarki Abdullahi II. A ranar Lahadi ake sa ran Merz ya gana da Firanminstan Isra'ila, Benjamin Netanyahu a birnin Kudus. Dangantaka ta yi tsami a tsakanin Jamus da Isra'ila a lokacin yakin Gaza, bayan da Merz ya yi kakkausar suka kan matakin soji da Isra'ila ke dauka a Gaza, wanda ya yi sanadin mutuwar Falasdinawa da dama. Kana a watan Augusta, Jamus ta rage yawan makaman da take siyar wa Isra'ila da take amfani da su a Gaza.

Karin bayani:Merz na Jamus ya caccaki Isra'ila bisa rikicin Gaza 

Sai dai tun bayan da aka cimma yarjejeniyar tsagaita bude wuta da ya kawo karshen yakin, Jamus din ta janye wannan takunkumin. Gabanin barinsa Jamus, Merz ya gana da shugaban Falasdinawa, Mahmood Abbas, inda jadda masa goyon baya ga samar da kasashe biyu masu cin gashin kansu.