Shugaban gwamnatin Jamus Merz zai gana da Trump
June 5, 2025
Nan gaba a wannan Alhamis shugaban gwamnatin Jamus Friedrich Merz zai gana da shugaba Donald Trump na Amurka a fadar White House a karon farko, inda ake sa ran za su tattauna game da sabon tsarin karin harajin Amurka ga kasashen duniya, da kuma batun tallafa wa Ukraine a yakinta da Rasha.
Mr Merz da ke jagorantar kasa mafi karfin tattalin arziki a Turai, zai yi ganawar ta keke-da-keke da Trump, wanda a baya bayan nan ya yi kaurin suna wajen kokarin tozarta shugabannin da yake karbar bakunci, la'akari da yadda ta wakana tsakaninsa da shugabannin Ukraine da Afirka ta Kudu, wannan ta sa hankali ya karkata kan yadda za ta wanye a wannan karo.
Karin bayai:Jamus: Kasashen duniya na taro kan tsaro a Munich
Hakan na zuwa ne makonni kalilan gabanin gudanar da babban taron kawancen kungiyar tsaro ta NATO, wadda Mr Trump ke barazanar janye wa tallafin tsaro, sakamakon zargin kasashen Turai da gaza bayar da tallafin kirki.