Olaf Scholz ya caccaki mai kamfanin X Elon Musk
January 4, 2025Shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz ya caccaki hamshakin attajirin nan mai kamfanin sada zumunta na X wato Elon Musk, da ya ayyana kalamansa a matsayin mara kan gado da tabbas, bayan da ya fito fili karara ya nuna goyon bayansa ga jam'iyyar AfD mai tsananin kyamar baki.
Karin bayani:Harin Magdeburg zai zama maudi'i a yakin neman zaben Jamus?
Mr Scholz ya ce baya neman duk kwata alfarma daga Musk da ke zama mafi arziki a duniya, kuma shi ba mai kin dimukuradiyya ba ne kamar yadda Elon Musk din ya bayyana shi a baya, har ya ce kamun ludayinsa na mulki ya nuna cewa bai cancanci jagorantar Jamus ba.
Karin bayani:Habeck ya gargadi Ellon Musk kan zaben Jamus
Shugaban na Jamus ya ce ya zabi kame bakinsa ne don ba da damar gudanar da babban zaben kasar na watan Fabarairu mai kamawa cikin kwanciyar hankali da lumana, kuma goyon bayan da Musk ya bai wa AfD ba zai kare ta da komai ba, face kara haddasa mata matsala.