Jamus ta taya sabon shugaban Romaniya murna
May 19, 2025
Shugaban gwamnatin Jamus, Friedrich Merz ya taya sabon shugaban kasar Romaniya Nicusor Dan magajin grin birnin Bucherest fadar gwamnatin kasar mai ra'ayin goyon bayan kasashen Turai murnar nasarar da ya samu a zaben da aka gudanar wannan Lahadi da ta gabata. Merz ya bayyyana haka a sakon da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta a kafar intanet.
Karin Bayani: Kotu ta sako sakamakon zaben Romaniya
Shugabanni da dama na Turai sun taya Nicusor Dan mai shekaru 55 murnar nasarar da ya samu da kaso 53 cikin 100 na kuri'un da aka kada, a gaban George Simion mai matsanancin ra'ayin mazan jiya wanda ya samu kaso 46 cikin 100 na kuri'un. Lokacin jawabin samun nasara zababben shugaban kasar Romaniya, Dan ya nuna cewa yana sane da gagarumin aikin da ke gaban-sa wajen inganta tattalin rzikin kasar da harkokin lafiya.
Galibin shugabannin kasashen Turai da suka hada da Ursula von der Leyen shugabar hukumar gudanarwar kungiyar da Shugaba Emmanuel Mcron na Faransa sun nuna gamsuwa da sakamakon zaben na Romaniya da mai ra'ayin goyon bayan kungiyar Tarayyar Turi ya samu galaba.