1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaban gwamnatin Mali ya bada tabbacin samun tsaro

Binta Aliyu Zurmi
April 29, 2026

Shugaban gwamnatin mulkin sojin Mali Assimi Goita ya bukaci al'ummar kasar da su kwantar da hankulansu, inda ya ba su tabbacin daidaituwar al'amura.

Russland Moskau 2025 | Assimi Goïta bei Unterzeichnung von Kooperationsabkommen
Hoto: Roman Naumov/Picvario Media/picture alliance

A jawabinsa na farko tun bayan harin da 'yan ta'adda da 'yan tawaye suka kai a karshen mako da ya girgiza gwamnatinsa, ya jaddada cewa an karfafa matakan tsaro kuma jami'an tsaro na ci gaba da kula da muhimman yankunan kasar. 

Wadannan bayanan na zuwa ne bayan shafe kwanaki uku ba a ji duriyarsa ba, lamarin da ya saka kokwanto a zukatan 'yan kasar kan shugabancinsa da ma samar musu da zaman lafiya.

Shugaban ya bukaci ‘yan kasar da su tashi tsaye su yi watsi da rarrabuwar kawuna yana mai cewa Mali na bukatar kwanciyar hankali, ba tsoro ba, don fuskantar kalubalen da take fuskanta. 

Ya kara da cewa hadin kan kasa yana da matukar muhimmanci a daidai lokacin da kasar ke fuskantar hare-hare daga kungiyoyi masu dauke da makamai.

Karin BayaniKo harin Mali zai zama ishara ga Nijar?