Shugaban gwamnatin Scotland ya yi murabus
April 29, 2024![Shugaban gwamnatin Scotand mai murabus Humza Yousaf](https://static.dw.com/image/65137895_800.webp)
Yousaf na fuskantar matsin lamba na yin murabus tun lokacin da jam'iyyarsa ta SNP ta yanke kawance da jam'iyyar Scottish Greens mai rahin kare muhalli a makon da ya gabata.
Karin bayani: Scotland za ta koma cikin kungiyar EU
'Yan adawa daga jam'iyyar Scottish Conservative sun sha alwashin kada kuri'ar yankar kauna kan ministan a ranar laraba, kafin ya yi murabus a wannan rana domin kauce wa mummunar hamayya daga mambobin majalisar.
Karin bayani: 'Yankin Scotland na neman ballewa daga Birtaniya
Yousaf shi ne musulmi na farko da ya jagoranci wata babbar jam'iyya a Burtaniya, wanda kafin zabarsa ya ke cike da fatan zai yi nasara.
Karin bayani: Scotland za ta ci gaba da zama a Birtaniya
Majalisar dokokin Scotland wadda aka sake kafa ta a 1999, na da takaitaccen ikon yin dokoki da suka shafi lafiya da ilmi da sufuri da kuma muhalli, yayin da gwamnatin Burtaniya a birnin Landan ke da karfin tasiri kan al'amuran da suka shafi kasa baki daya kamar tsaro da manufofin kasashen waje.