Shugaban gwamnatin tarayyar Jamus Angela Merkel, na ci gaba da ziyarar aikin da take kai wa ƙasar Sin.
May 22, 2006A ziyarar aikin da take kai wa ƙasar Sin, shugabar gwamnatin tarayyar Jamus Angela Merkel, ta gana da Firamiyan ƙasar Wen Jiabao. Wannan dai ita ce ziyarar Merkel ta farko a ƙasar Sin, tun da ta hau muƙaminta a cikin watan Nuwamban shekarar bara. Da take yi wa maneman labarai jawabi bayan ganawarta da Wen Jiabao, Angela Merkel ta bayyana cewa, ita da Firamiyan na Sin, sun yarje kan batun hana Iran mallakar makaman nukiliya. Sai dai, ba ta ce uffan ba, game da yiwuwar sanya wa Iran ɗin takunkumi. Ita dai Sin, ta sha nuna adawarta ga ɗaukar wani mataki na sanya wa birnin Teheran takunkumi, yayin da Jamus kuwa, kamar sauran ƙasashen Yamma, ke goyon bayan hakan.
Wata tawagar kasuwanci da ta ƙunshi mutum 40, a cikinsu har da ministocin tarayya biyu ne ke yi wa Merkel rakiya a ziyarar tata a ƙasar Sin.