shugaban hukumar jin kai na majalisar dinkin duniya ya isa Sudan
May 7, 2006Talla
Shugaban hukumar jin kai ta Majalisar Dinkin Duniya,Jan Egeland ya isa kasar Sudan,inda yayi kira da a baiwa maaikatan agaji karin damar shiga yankin Darfur,kamar yadda aka amince bisa yarjejeniyar kawo karshen yakin shekaru 3 a yankin.
Ana sa ran Egeland zai tattauna da gwamnatin Sudan wadda tayi alkawarin sake gina yankin na Darfur.
Karkashin yarjejeniyar ne kuma,zaa dauki yan tawaye 5,000 cikin rundunar tsaro ta Sudan.