Shugaban hukumar nukiliya ya isa Koriya ta arewa
March 13, 2007Talla
Shugaban hukumar hana yaduwara makaman nukiliya ta kasa da kasa Muhammad el-Baradei ya isa Pyongyang domin tattaunawa da shugabanin Koriya ta arewa tare da zummar samun izni ga supetocin hukumar sake komawa kasar.
A 2002 Koriya ta arewa ta kori supetocin hukumar ta hana yaduwar nukiliya bayan sabani data samu da Amurka.
Ziyarar ta El-Baradei tazo ne wata guda bayan muhimmiyar yarjejeniya da kasashe 6 masu tattauna batun nukiliya na Koriya suka samu ne,wanda ke nuni da cewa Koriya ta arewan zata dakatar da shirinta na nukiliya.
Karkashin yarjejeniya Pyongyang tace zata baiwa supetocin damar shiga kasar tare kuma da alkawarin rufe wata tasharta ta nukiliya cikin kwanaki 60 a madadin taimakon mai da zaa bata.