1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaban Iran na farko ya rasu

Abdul-raheem Hassan
October 9, 2021

Marigayi Banisadr ya rasu yana da shekaru 88 a duniya, ya kasance dan gwagwarmaya tun yana da shekaru 17, ya taba zama ministan tattalin arziki da harkokin waje na kasar Iran.

Iran Abdolhassan Banisadr
Hoto: Andreas Gebhard/dpa/picture-alliance

Shugaban kasar Iran na farko bayan juyin juya halin Musulunci a shekarar 1979, Abolhassan Banisadr ya rasu a wani asibiti a birnin Paris na kasar Faransa bayan doguwar jinya.

Marigayi Banisadr ya rasu yana da shekaru 88 a duniya, ya kasance dan gwagwarmaya tun yana da shekaru 17, ya taba zama ministan tattalin arziki da harkokin waje.

Mariyagayin ya zama shugaban kasa a watan Janairun 1980, sai dai majalisar dokokin Iran ta raba shi da kujerar shugabncin kasar a 1981 bayan ya yi adawa da marigayi jagoran addini Ayatollah Ruhollah Khomeini, matakin da ya tilasta shi yin hijira a Faransa.