1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaban Jamus na ziyarar aiki a wasu kasashen Afirka

November 2, 2025

Shugaban kasar Jamus Frank-Walter Steinmeier na ziyara a nahiyar Afirka, inda ya nuna damuwa kan halin da ake ciki a rikicin Gaza lokacin da yake jawabi a birnin Alkahira na Masar

Shugaban kasar Jamus  Frank-Walter Steinmeier tare da wasu 'yan asalin Afirka
Shugaban kasar Jamus Frank-Walter Steinmeier tare da wasu 'yan asalin AfirkaHoto: Britta Pedersen/dpa/picture alliance

Shugaban Jamus Frank-Walter Steinmeier ya bayyana damuwarsa kan halin da ake ciki a yankin Gabas ta Tsakiya, bayan ganawa da Firaministan Lebanon Nawaf Salam da kuma shugaban Masar Abdel-Fattah al-Sissi a birnin Alkahira a ranar Lahadi.

Steinmeier ya ce al'ummar yankin na fatan ci gaba da tattaunawar zaman lafiya a yankin Gaza, bayan yarjejeniyar dakatar da fada tsakanin Isra'ila da Hamas, duk da cewa da dama na nuna fargaba kan kalubalen da ke gaba.

Shugaban Jamus din yana cikin ziyarar kusan mako guda a nahiyar Afirka.

Kuma ya isa Masar a ranar Asabar, inda ya halarci bikin bude babban gidan adana kayan tarihi na Grand Egyptian Museum a birnin Alkahira.

A cewar fadar shugaban kasa ta Jamus, bayan ziyararsa a Masar, Shugaba Steinmeier zai wuce zuwa kasashen Ghana da Angola, inda yake da niyyar yaba da kokarin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali da wadannan kasashe ke yi a yankin yammacin Afirka.