SiyasaJamus
Shugaban Jamus na ziyarar Spain kan halin da Ukraine ke ciki
November 26, 2025
Talla
A wannan Laraba ce shugaban Jamus Frank-Walter Steinmeier ke ziyara kasar Spain, bisa rakiyar mai dakinsa Elke Büdenbender, inda zai samu tarba ta musamman daga sarki Felipe na shida, tare da sarauniya Letizia a birnin Madrid.
Daga bisani kuma shugaban zai gana da firaministan Spain Pedro Sánchez, inda za su tattauna kan muhimman batutuwa na yaukaka kyakkyawar alakar da ke tsakanin kasashen biyu, masu rajin kare bukatun kungiyar tarayyar Turai EU.
Karin bayani:Jamus za ta girka garkuwar sararin samaniya mai linzami
Batun da shugabannin biyu za su fi mayar da hankali a kai shi ne halin da Ukraine ke ciki sakamakon mamayar da take fuskanta daga Rasha, sai shirin nan na kaddamar da taron tattalin arziki tsakanin Jamus da Spain, na ranar Alhamis.