1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaban Jamus ya gana da mawallafa a Abuja

Uwais Abdubakar idris/USUFebruary 11, 2016

A ci gaba da ziyarar da yake yi a Najeriya shugaba Joachim Gauck ya gana da marubuta da masu wallafa litattafai a Abuja, tare da kira ga kasashen Afrika su maida hankali a yaki da ta’adanci.

Nigeria Gauck auf Staatsbesuch
Hoto: picture alliance/dpa/W. Kumm

Ganawar da shugaban na kasar Jamus ya yi da marubuta da masu wallafa litattafai a Abuja hedikwatar gwamnatin kasar dai, ta kasance matsayin karramawa ga wannan sashi na al’umma da ke taka rawa ta musamman wajen aikewa da sakwani don samun sauyi.


Sun kwashe tsawon lokaci suna tattaunawa da marubutan a asirce, inda suka tattauna batutuwa da suka shafi nau’i da tasirin wallafa litattafai da ma kasidu a Najeriyar, da hanyoyin da suke bi da zai kara sanya su samun kaimi da tasiri. Ko menene zahirin abubwan da shugaban na Jamus ya bayyana masu? Mr Ricahard Ali na cikin marubutan da suka hallarci taron.


‘’Mun yi magana kaman yadda ake rubutu a Najeriya da abubuwan da za su iya hana marubuta su yi hakan a cikin kwanciyar hankali. Abinda mun gane shi ne kasar Jamus ta dauki batun rubutu da wallafa litattafai da muhimmancin gaske, don haka ne da ya zo Najeriya ya zo don ya gana da mu’’


Ba kasafai shugabanin kasashen duniya da kan kawo ziyara ke kebe lokaci na musamman don ganawa da marubuta da mawallafa a cikin kasar ba, abin ya sanya laluben tasirin da wannan matsayi na shugaban na Jamus ya dauka zai yi, musamman ga marubuta da mawallafa na Najeriya. Mrs Safiya Ismail mai rubuta litattafai ce a kasar, wacce ta hallarci taron.

Hoto: picture-alliance/dpa/W. Kumm


‘’Na daya dai kaga idan alummar mu ta ji cewa wani shugaba ya zo har ya samu lokaci ya gana da mu wata kila zai sa sun dan waigo su san cewa fa eh, marubutanmu nan suna da muhimmanci. Domin kaga ba’a daukan marubuta da muhimmanci. Ni dai kaga bama shugaban kasa ba, ban ma taba ganawa da wani minista a Najeriya ba. Wannan ziyara da ya kawo mana a yanzu zai sa a fara daukanmu da dan muhimmanci’’


Tun kafin wannan dai sai da shugaban Gauck na Jamus ya kai ziyara a hedikwatar kungiyar kasashen Afrika ta Yamma wato Ecowas, inda ya bayyana bukatar aiki tare a fanin yaki da matsaloli na rashin tsaro da sauran kalubale tsakanin kungiyar Ecowas da Jamus, shugaba Gauck ya kara da cewa.


‘’Na yanke shawarar ganin mun yi aiki tare kusa da juna, don hada karfin tabbatar da cewa al'umma ta zauna cikin yanayin tsaro da zaman lafiya da kyayawar makoma. Wannan ya hada da batun kwararar bakin haure daga yankin Sahel zuwa kasashe da dama. Dole mu yaba a kan rawar da ma'aikatan agaji suka taka har da na kasar Jamus kun samu nasara kawar da cutar Ebola a yankin Afrika ta Yamma’’.


Shekaru 10 kenan dai Jamus na taimakawa kungiyar Ecowas a fanoni da dama, inda ta kashe sama da Euro milyan 22. Abinda ya sanya fatar ziyara da shugaba Gauck ke yi za ta kara yaukaka wannan danganta a tsakanin kungiyar kasashen yammacin Afrika da gwamnatin kasar Jamus.