1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Jamus na adawa da kyama da cin zali da sunan addini

Ramatu Garba Baba
October 30, 2020

Shugaban kasar Jamus Frank-Walter Steinmeier ya soki manufar kai hari kan jama'a da sunan addini inda ya nemi kasashen Turai da su tashi tsaye don dakile akidar cin zali da nuna kyama daga masu kaifin kishin Islama.

Halle | Gedenken an Anschlag auf Synagoge | Rede Bundespräsident Steinmeier
Hoto: Jan Woitas/dpa/picture alliance

Bayan harin birnin Nice na kasar Faransa da yayi sanadiyar rayukan mutum uku, Shugaban kasar Jamus Frank-Walter Steinmeier, ya soki manufar kai hari da sunan addini inda ya nemi kasashen Turai da su tashi tsaye don kawo karshen akidar cin zarafi da nuna kyama da sunan yin biyayya ga addini, Shugaban ya fadi hakan ne a yayin wata tattaunawa da yayi da tashar DW,  daga bisani, ya jajanta ma iyalan wadanda suka rasa ransu a harin na birnin Nice.

A daya bangaren kuma, dubban dubatan musulmi sun gudanar da zanga-zanga a kasashen Pakistan da Labanan da yankin Falisdinu a wannan Juma'ar don nuna adawa ga Shugaban Faransa. Gangamin na Pakistan ya koma tarzoma bayan da 'yan sanda suka yi amfani da hayaki mai saka kwalla a tarwatsa dandazon mutanen da suka yi yunkurin kutsawa cikin ofishin jakadancin Faransa da ke Islamabad. Al'ummar Musulmai sun nuna fushi ne kan kalaman Shugaba Emmanuel Macron na kare zanen batanci ga addinin Islama inda suka yi ta kira da a kaurace siyan kayayyakin Faransa.